Connect with us

News

Hukumar EFCC Ta Gayyaci Tsohuwar Ministar Jin-Kai Kan Badakalar 37bn

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Hukumar Yaki Da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), ta gayyaci tsohuwar ministar jin-kai, Sadiya Umar Farouk, kan zargin ta da karkatar da sama da Naira biliyan 37.

Hukumar ta bukaci Sadiya ta bayyana a hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Laraba mai zuwa don yin cikakken bayani game da yadda kudaden suka yi batan dabo.

Cikakken Jawabin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Ga Yan Najeriya Na Sabuwar Shekarar 2024

Sadiya Faruk na cikin ministocin Buhari da aka rika zargin su da cin hanci a lokacin da suke kan karagar mulki, duk da dai ta sha musanta zarge-zargen da ake yi mata.

Aminiya ta ruwaito cewa EFCC ta zargi Sadiya da hada kai da wani mutum mai suna James Okwete wajen wawure wadannan kudi, sai dai tuni tsohuwar ministar ta ce ko sunan mutumin ba ta taba ji ba.

Advertisement

Bayanai na nuna cewa James ya shafe kusan kwanaki 10 a hannun jami’an EFCC, inda suke gudanar da bincike a kansa.

Daga tsohuwar ministar har masu ba ta shawara da mataimakanta kan harkokin yada labarai sun ki yi wa manema labarai karin haske kan wannan lamarin.

Sai dai a wani sako da ta wallafa a shafinta na X a makon jiya, Sadiya ta ce ba ta taba sanin wani mai suna James Okwete ba, ballantana ta yi wata hulda da shi.

 

 

A baya-bayan nan dai an sha yin kira kan a binciki tsofaffin wadanda suka rike mukamai a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending