Connect with us

News

Malaman makarantu sun tsunduma yajin aiki a Nijar

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAH

Ƙungiyar malaman kananan makarantu ta “(SYNACEB) reshen Makalondi ta jihar Tillabery a Jamhuriyar Nijar ta tsunduma cikin wani yajin aiki.

Advertisement

Malaman sun shiga yajin aikin na kwanaki biyu ne daga ranar Litinin domin janyo hankalin gwamnati ta ɗauki matakai na kare malaman daga matsalar tsaro.

Mazauna garin Nahuta sun fice ba shiri, bayan dandazon ‘yan bindiga sun afka wa sansanin sojojin yankin Batsari

Ƙungiyar ta ce ɗauki matakin ne bayan la’akari da abin da ya faru a ranar 27 ga watan Oktoban bara, inda ‘yan bindiga suka yi awon gaba da wasu malaman makarantu biyu da kuma lamarin ranar 10 ga watan Janairu inda aka kashe wani malami bayan shafe tsawon lokaci a hannun ƴan bindigar.

Advertisement

Lamarin tsaro dai na ƙara taɓarɓarewa a jihar Tillabery duk da iƙirarin da shugaban majalisar mulkin sojin ƙasar yayi na cewa suna samun nasara a yaƙin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending