Connect with us

News

Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki Bayan An Farmake Su Bisa Zargin Sakaci Da Aiki 

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

 

Advertisement

Kungiyar Likitoci na asibitin koyarwa na jami’ar jihar Ekiti (EKSUTH) ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani kan harin da wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka kai a asibitin.

Leadership ta rahoto cewa, ‘yan daban sun kai farmaki asibitin ne a ranar Litinin bayan mutuwar wani mara lafiya da aka kawo asibitin a ranar Lahadi.

Advertisement

Wasu Mutane ‘Yan Kalilan Ne Suka Wawure Arzikin Najeriya Ta Hanyar Tallafi – Shugaba Tinubu

Acewar wata majiya, an kawo majinyacin asibitin ne a wani hali mawuwaci inda hakan yasa aka ajiye shi a sashin bayar da agajin gaggawa na asibitin amma duk da haka ya ce, ga garinku nan, ba a iya ceto rayuwarsa ba.

Rasuwar majinyacin ce ta fusata ‘yan uwansa, inda suka gayyato ‘yan daba suka farmaki likitocin tare da lalata dukiyoyi a asibitin saboda zargin da suka yi wa likitocin na sakaci da aiki.

Advertisement

An tura jami’an rundunar ‘yansandan jihar zuwa asibiti domin dawo da zaman lafiya da tsaron dukiyoyi amma dai kungiyar likitocin a zaman da ta yi na gaggawa, ta yanke hukuncin tsunduma yajin aiki, inda ta ce, “ana barazana ga lafiyar mambobinta”

A wani labarin kuma Wasu Mutane ‘Yan Kalilan Ne Suka Wawure Arzikin Najeriya Ta Hanyar Tallafi – Shugaba Tinubu

Advertisement

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

Advertisement

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

Advertisement

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Advertisement

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending