News
Shugaba Tinubu ya kashe fiye da kuɗin da aka ware masa wajen tafiye-tafiye – Rahotanni
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya kashe naira biliyan 3.4 a kan tafiye-tafiyen cikin gida da kuma na ƙasashen waje a cikin watanni shida na farkon mulkinsa, a cewar rahotanni.
Hakan na nufin Shugaba Tinubu da jami’an gwamnatinsa sun zarce kasafin kuɗin naira biliyan 2.49 da aka ware wa tafiye-tafiyensu a 2023 da kashi 36, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Punch ta ce duk da yake shugaban ya gaji kasafin kuɗin ne na rabin karshen shekarar 2023, “ya kashe sama da abin da aka ware a gaba-ɗaya shekarar daga watan Yuni zuwa Disamban 2023”.
Rahoton wanda BBC ba ta tabbatar ba, ya zo ne kusan mako ɗaya bayan da Shugaba Tinubu ya zaftare yawan jami’ai da za a bari suna yi masa rakiya yayin tafiye-tafiyensa da kuma na sauran manyan jami’an gwamnatinsa zuwa ƙasashen waje da kuma a cikin gida.
Kafin haka, an soki lamirin shugaban kan makudan kuɗaɗen da yake kashewa wajen tafiye-tafiye waɗanda ƴan Najeriya suke ganin sun yi yawa.
Ɗaya daga cikin tafiye-tafiyen ita ce, wadda gwamnatin Tinubu ta ɗauki nauyin jami’ai sama da 400 domin zuwa taron sauyin yanayi na COP28 da aka a yi Dubai, inda aka yi ta sukarsa.
A wani labarin kuma Dalilai 10 Da Suka Sa Gwamnatin Tinubu Ta Fi Ta Buhari
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
