Connect with us

News

Gwamnatin Kano Za Ta Kafa Gidauniyar Tallafawa Iyalan Sojojin Da suka Rasu

Published

on

Gwamnan jahar Kano Abba Kabir Yusuf

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ce, gwamnatinsa za ta kafa gidauniyar tattara kudade domin biyan bukatun iyalan jaruman da suka rasu a bakin aiki.

Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne a wajen bikin ranar tunawa da sojojin Nijeriya na shekarar 2024 da aka yi ranar Litinin a Kano.

Lionel Messi ya zama fitaccen ɗan kwallon kafa na Fifa

Ya ce, gwamnatinsa za ta gayyaci manyan mutane a jihar domin su mara wa gwamnati baya wajen kafa gidauniyar tallafawan.

A cewarsa, za kuma a yi amfani da gidauniyar wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar da samar da ayyukan yi ga matasa.

“Mun kuduri aniyar tabbatar da cewa, Jiharmu ta dore da zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma gwamnatinmu ba za ta bar komai a baya ba don aiwatar da wannan kyakkyawar aniyar,” in ji shi.

Advertisement

Da yake jawabi kan iyalan jaruman sojojin da suka rasu, gwamnan ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da fifiko wajen kyautata rayuwarsu.

Ya kuma bayyana cewa, iyalan jaruman da suka rasu, za su ci gajiyar tallafin da za a raba wa al’ummar jihar.

Gwamnan ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da hada kai da jami’an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

A wani labarin kuma Lionel Messi ya zama fitaccen ɗan kwallon kafa na Fifa

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

Advertisement

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending