News
Jikan Sardauna, Magajin Garin Sokoto ya rasu
Daga yasir sani abdullahi
Allah Ya yi wa Magajin Garin Sokoto, Alhaji Hassan Marafa Danbaba rasuwa a ranar Asabar a Kaduna bayan gajeruwar rashin lafiya.
Wani babban aminin marigayin ne ya tabbatar wa BBC da rasuwar Magajin Garin.
Ana sa ran za a yi janai’zar mamacin a ranar Asabar a birnin Sokoto.
Marigayin ya kasance ɗa ga Aishatu Ahmadu Bello, wadda ƴa ce ga Sardauna Ahmadu Bello.
Alhaji Hassan Marafa ne Magajin Garin Sokoto na 13 kuma an naɗa shi ne a ranar 31 ga watan Oktoban 1997
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News5 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
