News
NDLEA ta kama wata mace Mai ciki da Safar miyagun kwayoyi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Jami’an Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Nijeriya wato NDLEA sun kama wani mutum mai shekaru 42 da aka ce yana jigilar dubunnan miyagun kwayoyin na Opiod a boye zuwa wani yanki na ‘yan tada kayar baya a yankin Banki na Jihar Borno.
Wanda ake zargin dai yana cikin mutane 24 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a fadin kasar, a cewar kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata.
Sanarwar ta ce a sumamen da aka yi sun kai ga kama wasu miyagun kwayoyi daban-daban da ya kai kilogiram 7,609 a jihohi takwas.
Haka kuma an kama wata mace mai cikin wata shida, mahaifiyar ‘ya’ya uku, da kuma wasu mata uku a cikin wasu manyan samamen.
A cewar sanarwar, an kama mafi yawan masu jigilar kwayoyin ne a Jihar Nasarawa inda jami’an hukumar NDLEA da ke aiki bisa sahihan bayanan sirri, a watan Fabrairu, suka kama wata mota da lambar Legas JJJ 64 YC dauke da buhunan tabar wiwi guda 367 mai nauyin kilogiram 4,037 daga Akure, Babban Birnin Jihar Ondo, wanda za a kai a yankin Shabu da ke Lafia, babban birnin jihar.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
