Connect with us

News

Da dumi dumi _Sojojin Nigeria sunyi nasarar kashe ƴan ta’adda 254 a wasu sassan jahohi

Published

on

Sojojin Nigeria

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

 

Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta ce sojojin ƙasar ta sun yi nasarar kashe ƴan ta’adda 254 da kuma kama 264 a cikin mako guda a faɗin ƙasar.

 

Daraktan watsa labarai na hedikwatar tsaron Manjo Janar Edward Buba ne ya tabbatar da hakan a wani taron watsa labarai a ranar Juma’a.

Advertisement

Ya bayyana cewa a samamen da jami’an tsaron suka kai a faɗin ƙasar, sun ceto mutum 73 waɗanda aka yi garkuwa da su.

A yankin kudu maso kudancin Nijeriya, sojojin ƙasar sun samu nasarar ƙwato gangar mai 20,643 daga hannun ɓarayin mai wanda kuɗin man ya kai kimanin naira biliyan 2.6.

Sojojin sun ce duk a cikin mako guda, sun yi nasarar ƙwato makamai 5,083 daga hannun ƴan ta’addan da kuma tsabar kuɗi naira 748,430.

Sauran abubuwan da aka ƙwato sun haɗa da motoci 18 da babura 40 da wayoyin hannu 74 da ɗumbin harsasai da bindigogi.
Matsalar tsaro a Nijeriya na ƙara ƙamari duk da jami’an tsaron ƙasar suna iƙirarin samun nasara.

Domin ko a cikin makon nan sai da sojojin ƙasar suka ce sun gano wani waje da ake ƙera makamai a Jihar Filato tare da gano tarin makamai da harsasai. Kamar Yadda TRT Africa ta rawaito

Haka kuma a makon da ya gabata sojojin sun ce sun kama wani kasurgumin dan bindiga da ake nema wanda yake da hannu a safarar makamai ga masu laifi a jihar Taraba da ma wasu sassan kasar.

Advertisement

Arewa maso gabashin Nijeriya da kuma arewa maso yammacin Nijeriya na daga cikin wuraren da ƴan ta’adda suka fi addaba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending