News
Zamu sadukar da kanmu Domin cigaban Nigeria -sarkin gwandu na kebbi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Sarkin Gwandu na Kebbi, Muhammadu Iliyasu-Bashar, ya bukaci ‘yan Najeriya da su nuna kishin kasa don bunkasa zaman lafiya da hadin kai a kasar.
Kebbi Ya bayyana haka ne a yayin wani liyafa da aka shirya don karrama mataimakin shugaban jami’ar Fatakwal, Farfesa Georgewill Owunary, a fadarsa da ke Birnin Kebbi ranar Asabar dinnan kamar Yadda gidan jaridar solace base ya rawaito
Shugaban Majalisar Sarakunan Kebbi ya ce “kasar nan tamu ce, don haka dole mu dauki kanmu a matsayin ‘yan uwa. Najeriya babbar kasa ce kuma tana dauke da abubuwa da yawa, Kuma dole ne mu sadaukar da kai don ganin ta kasance daya.”
Adan haka zamu cigaba da jagorantar Al,umma Kuma zamu cigaba dasa ido a fannoni domin ganin kasar mun dorata a tudun mun tsira Kuma mun gudu tare mun tsira tare
