Connect with us

Business

Kudin Nijeriya Ya Karye Zuwa ₦2,000 Daidai Da Fam 1 Na Burtaniya

Published

on

 

Kudin Nijeriya a kasuwar musayar kudi ta bayan-fage ta karye, inda Naira 2,000 take daidi da Fam 1 na Burtaniya.

Wani Mai canjin kudi a kasuwar ‘yan canji ta Wuse Zone 4 da ke Abuja, Malam Ibrahim, ne ya tabbatar wa da jaridar PUNCH da farashin a yau ranar Litinin.

Da Ɗumi-ɗumi: Tsohon Gwamnan Kwara Ya Faɗa Komar Hukumar EFCC

Da aka tambaye shi game da canjin, sai ya ce, Eh gaskiya ne, a halin yanzu muna canzar da sama da Naira 2,000 akan fam 1,kuma har yanzu ana kan bukatar wadannan kudaden.”

Sabon farashin ya karu daga Naira 1,930 da aka samu a ranar Asabar, kuma a halin yanzu shi ne mafi karanci a tarihin Naira.

Kazalika, darajar Naira ta yi fadi idan aka kwatanta da dala a kasuwar hada-hadar hannayen jari, inda ba a hukumance ba a kan same ta a N1,673 daga N1,670/$ a ranar Juma’a.

Advertisement

Ana ci gaba da samun wannan duk da yadda babban bankin Nijeriya ya aiwatar da wasu sauye-sauye da dama da nufin karfafa samar da kudaden waje.

Daya daga cikin sauye-sauye a baya-bayan nan shi ne sanarwar da CBN ta bayar na dakatar da kamfanonin mai na kasa da kasa da ke aiki a Nijeriya daga gaggauta tura kashi 100 na kudaden da suke samu ga kamfanoninsu a kasashen waje.

Manazarta kasuwar sun danganta koma bayan da aka samu a baya-bayan nan ga karuwar bukatar daloli tun farkon watan Janairu.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending