News
Gwamnatin Tarayya Za Ta Zartar Da Dokar Karya Farashin Magunguna
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammed Ali Pate, ya bayyana cewa, nan ba da dadewa ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai rattaba hannu kan wata doka domin rage tsadar magunguna da kayayyakin kiwon lafiya.
Leadership ta ruwaito cewa Ministan ya bayyana haka ne a ranar Laraba a wani taron manema labarai na ministoci wanda ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mista Mohammed Idris, ke jagoranta a Abuja.
An Dakatar Da Cristiano Ronaldo Daga Buga Wasa Saboda ‘Rashin Ɗa’a’
Yayin da yake bayyana irin gagarumin ci gaban da aka samu a fannin kiwon lafiya karkashin gwamnatin shugaba Ahmed Bola Tinubu tun daga watan Mayun shekarar 2023, Pate ya ce, duk da ficewar da manyan kamfanonin magunguna na duniya suka yi daga kasar, gwamnati ta dukufa wajen rage tsadar magunguna da kayayyakin kiwon lafiya a kasar nan.
Ya ce, “wata doka ta Shugaba Tinubu na nan tafe don rage tsadar magunguna da kayayyakin kiwon lafiya a kasar nan.”
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
