Connect with us

News

Ku yi wa ma’aikata ƙarin albashi don ba su walwala —Ƙungiyar Ƙwadago NLC

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta ce ya zama wajibi gwamnati a dukkanin matakai ta yi ƙarin albashi domin bai wa ma’aikata damar yin rayuwa daidai da halin da ƙasa ke ciki.

Shugaban NLC na Ƙasa Joe Ajaero, shi ne ya bayyana haka a wajen taron da ƙungiyar ma’aikatan lafiya ta shirya a ƙarshen mako a Abuja.

Gwamnati Ta Kafa Dokar Hana Amfani Da Mazubin ‘Take Away’

A ranar Alhamis da ta gabata NLC ta bayyana N709, 000 don a amince da shi a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata a faɗin a ƙasar.

A hannu guda, takwararta, TUC kuwa, N447,000 take hari ya zama mafi ƙarcin albashi ga mambobinta a faɗin ƙasa.

Ajaero ya ce a halin da ake ciki, an maida ma’aikata sun zama maroƙa ƙarfi da yaji saboda tsadar rayuwar da ake fama da ita.

Advertisement

Ya ce, “Abinci ya yi ƙaranci ta yadda ‘yan Nijeriya sun koma tsintar abin da za su ci a juji da kai wa motocin ɗaukar kaya farmaki da wawashe rumbun ajiya don neman abinci.

“Idan waɗanda ke riƙe da gwamnati ba sa ganin wannan bala’in da ke faruwa, mu muna gani kuma za mu tabbatar da gwamnati ta sauke haƙƙoƙin jama’a.

“Kullum yunwa ƙaruwa take a ƙasarmu, kuma ba zai yiwu mu ci gaba a haka ba. Rainin hankali ne idan waɗanda ke gwamnati na zaton masu zanga-zanga don nuna rashin jin daɗinsu, ɗaukar nauyinsu aka yi.”

A ƙarshe Shugaban na NLC ya ce, masu ganin barazanarsu za ta iya hana su ci gaba da gwagwarmayar da suke yi, su sake tunani.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending