News
Dubun Wani Gardi Ya Cika,An Kama Shi A Ɗakin Kwanan Ɗalibai A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Jami’an Civil Defence’ reshen jihar Kano sun Yi nasarar damƙe wani gardi mai suna Muhammad Munzali ɗan garin Ƙaura Gidan Damo a ƙaramar hukumar Shanono.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar NSCDC, Ibrahim Abdullahi,shi ne ya tabbatar da kamen a yau Juma’a.
Ya ce Jami’an sun damƙe wanda ake zargin ne da misalin karfe 10 na dare a ranar Laraba a lokacin da yake ƙoƙarin kutsawa cikin ɗakin kwanan ɗaliban na jami’ar Skyline wanda ke kan titin Sardauna Crescent, Nassarawa GRA,Kano
“Wanda ake zargin yayi ɓadda kama da shigar mata inda yayi ƙoƙarin kutsawa ɗakin kwanan ɗaliban,Ko Da aka cafke shi an same shi da layu a jikin sa,” cewar PRO .
A Cewar Ibrahim zuwa yanzu ana cigaba da gudanar da bincike domin gano hujjar sa na yin wannan kutse inda daga nan ne za a san wani mataki za a ɗauka.
-
News1 day ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News4 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
