News
Matsalar intanet a Najeriya da wasu ƙasashe zai iya shafe wata ɗaya ana fama nan gaba – Mainone
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
An sanar da cewa gagarimin aikin gyaran wayoyin kebul na intanet da ke ƙarƙashin ruwan teku, wanda lalacewar su ya kawo matsalar intanet a Najeriya da wasu ƙasashen Afrika, zai iya kai makonni biyar ana faman gyara nan gaba.
Kamfanin MainOne, wanda shi ne ke samar da data wadda ake buɗe intanet da ita ƙasashen Afrika ta Yamma da ƙasashen Kudancin Afrika, shi ne ya bayyana haka a ranar Juma’a.
A cikin sanarwar ta ranar Juma’a, MainOne ya kuma yi ƙarin bayani dangane da katsewar da wayoyin kebul ɗin suka yi a ƙarƙashin teku, sai kuma bayanin irin ƙoƙarin gyaran da ake kan yi.
Cikin sanarwar da kamfanin ya bayar a shafin sa na intanet, ya ce: “Wayoyin kebul ɗin intanet na MaiOne da ke ƙarƙashin teku su na kai saƙonni ƙasashen Afrika da dama shi ya sa hakan ta faru.”
Premium Times ta ruwaito cewa MainOne ya ce sun rattaba yarjejeniyar gyara da kamfanin Atlantic Cable Maintenance and Repair Agreement (ACMA), domin ya gyara kebul ɗin can a ƙarƙashin ruwan teku.”
Sanarwar ta ce matakin farko shi ne a samu jirgin da zai yi ninƙaya a ƙarƙashin ruwa, domin ya gano ainihin wayoyin da suka katse, sai kuma gano daidai wuraren da za a yi gyaran.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
