News
An Kubutar Da Almajirai 18 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Sokoto
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Kimanin makonni biyu da suka gabata ne aka ‘yan bindiga suka sace yaran su 16 a wata makatrantar Almajirai da ke kauyen Gidan Bakuso a yankin Kaeamae Hukumar Gada.
Dan Majalisar Dokoki ta jihar Sakkwato mai wakiltar mazabar Gada ta gabas Honorabul Haruna Dauda ya ce an ceto yaran ne bisa ga kokarin mai baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu da hadin guiwar gwamnatin jihar Sokoto.
Yace Kwamandan garison na sojojin Najeriya dake Sokoto ne ya hannunta yaran da wasu mata da aka ceto su goma sha takwas.
Ramadan: Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi umarni a binciki masu raba abincin azumi
A cewarsa, Gwamnan Sokoto, Ahmad Aliyu, ya umurci a duba lafiyar mutanen da aka ceto kuma dukkansu na cikin koshin lafiya.
Muryar Amurka ta ruwaito cewa Gwamnatin Sokoto daga bisani ta hannunta mutanen ga Shugaban karamar hukumar Gada da sauran shugabannin yankin domin a sadar da su da iyalansu.
Ranar Jumu’a, 8 ga watan Maris ne ‘yan bindigar suka kai samame suka sace almajiran da wasu mata a kauyen Gidan Bakuso a karamar hukumar Gada dake gabasin Jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya.
