News
A DUMI-DUMI: Yan bindiga Sun Saki Wakilin Gidan Talabijin Na Channels Da Aka Sace
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wakilin gidan Talabijin na Channels, Joshua Rogers, da aka yi garkuwa da shi a jihar Ribas ya shaki iska ‘yanci.
An yi garkuwa da Rogers ne a daren ranar Alhamis da misalin karfe 9 na dare bayan da aka ce an bi sawunsa zuwa gidansa.
Kasar Iran ta fito da ‘makamai masu linzami fiye da 100’ don kai wa Isra’ila hari
Rahotanni na nuni da cewa maharan suna dauke da bindiga, inda suka tafi da shi a cikin motarsa.
DAILY POST ta ruwaito cewa barayin sun tuntubi matarsa, inda suka bukaci a biya su Naira miliyan 30.
Sa’o’i kadan da faruwar lamarin, sace Rogers ya mamaye kafafen yada labarai, inda kungiyoyi daban-daban ke kira da a sake shi ba tare da wani sharadi ba.
Ba a bayyana ko an biya wani kudin fansa domin a sake shi ba.
An hango shi a gidan babban yayansa tare da sauran ’yan uwa da abokan arziki suna Allah godiya.
Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ba ta bayar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
