Connect with us

News

Ana Hasashen Cewa Ambaliyar Ruwa Za Ta Shafi Jihohin Nijeriya 31 a daminar bana

Published

on

DAFA YASIR SANI ABDULLAHI 

Farfesa Joseph Utsev, Ministan Albarkatun Ruwa da Tsaftar muhalli, ya yi gargadin cewa kananan hukumomi 148 a fadin jihohi 31 na daga cikin wuraren da Za,a  iya fuskantar barazanar ambaliyar ruwa  a shekarar 2024.

Utsev ya yi wannan gargadin ne a lokacin da yake kaddamar da shirin na shekara ta 2024 na ambaliya ruwa (AFO) a ranar Litinin a Abuja.

Kungiyoyin  Ƙwadago Sun Bukaci Gwamnati Ta Biya Ma’aikata ₦615,000 A Matsayin Mafi Karancin Albashi

Taken AFO na wannan shekara shine “Haɓaka Amfani da Tattalin Arziki da Samfura don Ƙididdigar Hadarin Ambaliyar Ruwa da Tsaron Abinci.”

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa Hukumar Kula da Ruwa ta Najeriya (NIHSA) ce ke jagorantar hasashen AFO na kowace shekara.

Jihohin da aka gano sune: Adamawa, Akwa-Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross-River, Delta, Ebonyi, Edo, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi da Kogi.

Advertisement

Sauran sune: Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Plateau, Rivers, Sokoto, Taraba, da Yobe.

Utsev ya jaddada mahimmancin matakan da za a dauka don rage tasirin ambaliyar ruwa a wadannan yankuna.

Ya ce akwai bukatar a yi shiri, da tsarin gargadin wuri, da hada-hadar jama’a domin rage barnar rayuka da dukiyoyi.

 

Tun da farko, Farfesa Charles Anosike, Darakta Janar na Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NIMET), ya ce hadin gwiwar da ke tsakanin NIHSA da kungiyarsa na da matukar muhimmanci wajen bunkasa shirin bala’o’i a kasar.

Zubaida Umar, Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ta jaddada bukatar gaggauta daukar matakan dakile illar ambaliya a fadin kasar nan.

Advertisement

A nasa bangaren, Clement Nze, Darakta-Janar na NIHSA, ya jaddada muhimmiyar rawa na karfafa haɗin gwiwa tsakanin masu kula da hadarin bala’i, masu lura da duniya, masu yin manufa, da sauran masu ruwa da tsaki don haɓaka shirye-shirye da matakan magance ambaliyar ruwa.

 

 

Solace base 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending