Connect with us

News

Emefiele Ya Kalubalancin Hurumin Kotun Jihar Legas Na Sauraron Shari’arsa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ya bayyana cewar babu wata kotun jiha a Najeriya da zata iya sauraron shari’ar da ake yi masa kan zargin cin amanar mukami kasancewar hakan zai iya bijiro da batun dacewar hakan bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulki dana shari’a.

Advertisement

Muryar Amurka ta ruwaito cewa Babbar Kotun Jihar Legas dake zamanta a Ikeja ta jinkirta yanke hukunci har sai nan gaba game da karar da tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya shigar yana kalubalantar huruminta na sauraron shari’arsa akan tuhume-tuhumen Da Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya ke yi masa.

JAMB Ta Rike Sakamakon Jarabawar Dalibai 64,624 Tare Soke Lasisin Wata Cibiyar Jarabawarta A Kano

Ta hannun lauyansa kuma Babban Lauyan Najeriya, Olalekan-Ojo, Emefiele ya bayyana cewar babu wata babbar kotun jiha dake da hurumin yi masa shari’a a bisa tuhumar cin amanar mukami saboda hakan zai bijiro da batutuwan tanade-tanaden kundin tsarin mulki dana shari’a.

Advertisement

Tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriyar ya kara da cewar tuhuma ta 1 zuwa ta 4 daga cikin tuhume-tuhume 26 da Hukumar efcc ke yi masa sun sabawa kundin tsarin mulki kuma basa cikin dokokin najeriya.

Saidai EFCC ta bakin lauyanta wanda shima Babban Lauyan Najeriya ne, Rotimi Oyedepo ta kalubalanci hujjojin.

Advertisement

Ta hanyar kafa hujja ta hukunce-hukuncen da Kotun Kolin Najeriya ta yanke, Oyedepo ya bukaci alkalin kotun, Mai Shari’a Rahman Oshodi, da kada ya jinkirta ko dakatar da shari’ar a bisa la’akari da kalubalantar wasu daga cikin tuhume-tuhumen da ake magana akai.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending