Connect with us

News

Kotu Ta Hana DSS Cigaba Da Tsare Dakataccen Gwamnan Babban Bankin kasa Godwin Emefiele

Published

on

DSS/Godwin Emefiele

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Wata bababr kotun taraiyya dake zamanta a Abuja tayi watsi da bukatar Hukumar tsaro ta farin kaya DSS wadda ke neman a bata damar ci gaba da tsare dakataccen gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele har nan da makwanni biyu masu zuwa.

Mai shari’a Hamza Mu’azu ya baiyana bukatar a matsayin cin fuska ga hurumin da kotun ke da shi.

Advertisement

Hukumar ta DSS ta karkashin lauyoyin sun shigar da karar ne gaban kotu saboda wasu hujjoji da suka gabatar.

Mutane 130 Sun Kamu Da Cutar Mashako A Kano

Sabuwar bukatar da hukumar tsaro ta farin kayan ta shigar ta biyo sake damke Godwin Emefiele da ta yi a harabar babbar kotun taraiyya dake Legas, wadda ta bada umarnin cigaba da tsare shi a gidan gyaran hali, zuwa lokacin da zai cika sharuddan bada shi beli.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending