Sports
Kungiyoyin Da Ke Doka Gasar Premier Za Su Kaɗa Ƙuri’a Kan Bukatar Soke Na’urar VAR
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Kungiyoyin da ke doka gasar Premier sun shirya kada kuri’a kan ko za su soke na’urar taimawa alkalin wasa ta VAR ko ci gaba da amfani da ita yayin taron masu hannun jarin Klub Klub din a wata mai zuwa gabanin kakar wasa mai kamawa.
Majalisar Dattawa Ta Amince Wa Tinubu Ciyo Bashin $500m Don Sayen Mitocin Lantarki
Alkalin wasa Wilmar Roldan yayin nazartar na’urar VAR taimaka wa alkalin wasa da maimaicin hoton bidiyon da ta nada.
Kungiyar Wolves ce ta gabatar da shawarar, tare da kungiyoyin Midlands saboda rashin gamsuwarsu da wasu hukunce hukunce ko kura kurai da VAR ta tafka a kakar wasa ta bana.
Dole kungiyoyi 14 su kada kuri’ar amincewa da matakin soke VAR don jingine fasahar a kakar wasa ta 2024-25.
Tun bayan da aka fara amfani da fasahar a gasar Premier shekaru biyar da suka gabata, VAR ta raba kan kungiyoyi tare da haifar da rudani tsakanin magoya baya kan ko ta inganta.
Akwai wasu hukunce hukuncen VAR 6 da suka firgita duniyar kwallo cikin watanni 12 da suka gabata wanda ya haifar da gagarumar muhawara.
An kirkiri na’urar ce, saboda kura kurai da dan adam ke yi, amma, har yanzu alkalan wasa sun ci gaba da tafka kura-kurai.
Basa aiki da ainihin abin da suka gani a hotun, sannan wani lokaci ko yan wasa sun ja hankalinsu su je suka kallo sai su tsaya kan matsayarsu a ci gaba da wasa.
Fri
-
News5 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
