Connect with us

News

Mahaifi Ya Kai Ɗansa Kotu Domin A Yanke Masa Hukuncin Ɗaurin Rai-da-rai A Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Wani fusataccen mahaifi ya yi ƙarar dan cikinsa a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano.

Mahaifin ya koka da cewa ɗan nasa ya addabar shi da sace- sace da kuma shaye-shaye.

Nijeriya Da Jamhuriyar Benin Za Su Sassauta Tsanantawa A Kan Iyakokinsu Ga ‘Yan Kasuwa

Mahaifin, wanda aka boye sunansa ya nemi kotun ta ɗaure ɗan nasa har illah ma sha Allah.

Mai gabatar da kara, Abdul Wada, ya karanta wa wanda ake ƙarar tuhume-tuhumen da ake masa, inda nan take ya amsa laifinsa.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Malam Umar l Lawan Abubakar, ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Yuni 2024 don yanke hukunci.

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending