News
Da Dumi-Dumi: Gwamnan Kano ya bayar da umarnin tsare tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero cikin gaggawa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya bayar da umarnin tsare tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero cikin gaggawa.
A wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawunsa ya fitar a madadinsa, Yusuf ya zargi Ado Bayero da haifar da tashin hankali a jihar.
Ana zargin dawo da Aminu Ado Bayero cikin Masarautar Kano da sanyin safiyar Asabar din nan bayan tube rawaninsa da aka yi aka mayar wa da Muhammad Sanusi
Wata majiya daga filin jirgin sama na Malam Aminu Kano ta shaida wa jaridar Daily Nigerian cewa an jibge jami’an tsaro masu tarin yawa da za su tsare lafiyar tsohon Sarkin na Kano Aminu Ado Bayero a fadar sarkin Kano da aka kudiri aniyar mayar da shi.
Kungiyar Kwallon Kafa Ta Barcelona Ta Yanke Shawarar Korar Kocinta Xavi
Jaridar ta wallafa cewa shi ma sabon Sarkin na Kano Muhammd Sanusi ya yi gaggawa tarewa a fadar don dakile yunkurin dawo da tsohon sarki Aminu. Ana dai zargin Gwamnatin tarayya da hannu a kitsa kokarin dawo da tsohon sarki Aminu kamar yadda Daily Nigerian ta ba da labari.
-
News6 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News5 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
-
News6 days ago
Musa Illiyasu Kwankwaso Ya Taya Sanata Lado Murnar Cika Shekaru 60, Ya Kira Shi Gogaggen Ɗan Siyasa

