Connect with us

News

Wani mahajjati dan Jahar kebbi ya rasu a kasa Mai tsarki

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Wani alhaji Dan asalin Jahar Kebbi ya rasu bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya a birnin Makka na kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa marigayin, Alhaji Muhammad Suleman, ya fito ne daga karamar hukumar Argungu Kuma , ya rasu ne a ranar Lahadin da ta gabata bayan gajeruwar rashin lafiya.

Advertisement

Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kebbi, Alhaji Faruku Aliyu-Enabo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Makka ranar Lahadi.

Yace: “Marigayin ya rasu ne a ranar Lahadin da ta gabata bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya, kuma an yi sallar jana’izarsa a masallacin Al-Haram (Ka’aba).

Advertisement

“An yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a wannan rana.
“A madadin gwamnatin Kebbi, ina mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalansa da alhazan Kebbi da daukacin al’ummar jihar baki daya.

“Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta masa kurakuransa, Ya kuma jikansa da rayukan Musulmin da suka rasu, Ka sakasu a cikin Al,Jannatul Firdausi.”

Advertisement

Shugaban ya bukaci iyalan marigayin da su kwantar da hankalinsu tare da amincewa da yardar Allah Ta’ala cikin aminci, tare da lura da cewa babu wani rai da zai wuce lokacin da aka ayyana.

Idan za,a iya tunawa dai jaridar inda ranka ta rawaito cewa hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kebbi a ranar Lahadin da ta gabata ta sanar da rasuwar daya daga cikin mahajjatan ta mai suna Tawalkatu Busare Alako daga karamar hukumar Jega.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending