News
Yan bindiga sun fimu samun bayanan sirri _gwamnatin Jahar Katsina
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan jihar Katsina, alhaji umar radda ya ce suna fuskantar matsala a yakin da suke da yanbindiga saboda “suna samun bayanai fiye da yadda gwamnatin ita karanta take samu”.
Radda ya faɗi hakan ne a wani taron manema labaru da ya gabatar a Katsina, babban birnin jihar.
Gwamnan yace Katsina na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fuskantar matsalar ƴan bindiga masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.
Kuma ana ganin cewa matsalar tana ƙamari sanadiyyar mutanen da ke kwarmata wa ƴan bindigar bayanan sirri al’umma.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya ce suna fuskantar matsala a yakin da suke da yanbindiga saboda “suna samun bayanai fiye da yadda muke samu”.
Dikko ya ce: “Makahon yaki ne ake yi da yan bindiga saboda ba ka sanin waye makiyinka ko masoyinka saboda wani lokaci duk da masu ba su bayanai muke tare saboda haka kowa sai ya zama ɗan sandan kan shi wajen samar da tsaro.
“Muna tattaunawa kan matsalar tsaro amman muna gamawa za su samu dukkan bayanan da muka tattauna”.
Gwamna Radda ya ce har yanzu yana kan bakansa na cewa kowane bangare yana da hannu cikin rashin tsaro a Najeriya. “Mun kama sarakai da jami’an gwamnati da ke da hannu cikin matsalar tsaro a jihar Katsina, mun kuma samu bayanai da dama dake tabbatar da hakan”.
