Connect with us

News

Abubuwa 10 Da Ya Kamata Ku Sani A Safiyar Wannan Ranar Lahadi 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

1. Shugaban kasa Bola Tinubu ya gargadi kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke kai wa sojojin hari, inda ya ce Najeriya na da karfin da za ta iya magance su. Da yake mayar da martani kan kisan da aka yi wa sojoji a garin Aba na jihar Abia, kwanaki biyu da suka gabata, shugaban ya yi nadamar cewa wannan harin ya faru ne watanni biyu bayan na Okuama a jihar Delta.

Advertisement

2. Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), a ranar Asabar din da ta gabata, ya fitar da sunayen kwastomomi 25 da suka hada da wasu hukumomin gwamnati da su ke bin kudaden wutar lantarki. A cikin sanarwar, DisCo ta ce za ta katsewa duk abokan cinikin da suka kasa biyan basussukan su nan da ranar 3 ga watan Yuni.

Yadda Dagaci ya karbi N700,000 ya bari ‘yan bindiga suka kashe jama’a masu yawa a kauyensa

3. Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ce abin da kasar nan ke bukata shi ne shugabanci na gari, ba wai a sauya tsarin mulki ba kamar yadda ake ta kururuwa a wasu bangarori. Mataimakin shugaban kasar ya yi wannan jawabi ne a wajen bikin cika shekaru 30 na Yusuf Ali & Co (Ghalib chambers) a Ilọrin, babban birnin jihar Kwara, ranar Asabar.

Advertisement

4. Gwamnatin tarayya ta bayyana bukatar kungiyar kwadago ta kasa na neman karin mafi karancin albashi na N494,000 a matsayin rashin dorewar tattalin arziki, tana mai gargadin hakan na iya gurgunta tattalin arzikin kasar tare da yin illa ga sama da ‘yan Najeriya miliyan 200. Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a Abuja.

5. Darakta-Janar na kungiyar masana’antu ta Najeriya, Ajayi Kadri, ya tabbatar da cewa kamfanoni masu zaman kansu sun amince da kudurin gwamnatin tarayya na sabon mafi karancin albashi na N60,000. Ajayi ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels TV a Abuja ranar Asabar.

Advertisement

 

6. Kungiyar ma’aikatan man Fetur da iskar Gas ta Najeriya NUPENG a ranar Asabar din da ta gabata ta umurci mambobinta da su bi yajin aikin sai baba-ta-gani da kungiyar kwadago ta bayar da umarnin yi a fadin kasar. Yajin aikin da kungiyar kwadagon ta ayyana don matsawa kan bukatar mafi karancin albashin ma’aikata, zai fara aiki ne a ranar Litinin mai zuwa.

Advertisement

7. Jimillar ‘yan takara 70,608, a ranar Asabar, sun zana jarrabawar gama gari ta bana, NCEE, a fadin kasar nan. Sai dai adadin wadanda suka yi rajista ya yi kasa da na shekarar 2023, inda sama da ‘yan takara 72,000 suka yi rajista tare da shiga aikin.

8. Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana a ranar Asabar cewa Najeriya na kara samun rudani, rashin tabbas da sarkakiya. Ya kara da cewa rashin tsaro ya sanya kasar ta zama wuri mai hadari, cike da wahala da yunwa. A gare shi, dole ne shugabanci ya farka daga nauyin da ya rataya a wuyansa domin samar da ingantacciyar duniya ga dukkan ‘yan Najeriya.

Advertisement

9. Shugaban jam’iyyar, NNPP reshen jihar Kano, Hashimu Dungurawa, ya bayyana a matsayin rashin gaskiya a rahoton da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa, EFCC, ta fara bincike a kan kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa, wanda shi Rabiu Musa Kwankwaso ke jagoranta. Dungurawa, yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano, ya dage cewa rahoton jita-jita ce maras tushe.

10. Real Madrid ta lallasa Borussia Dortmund da ci 2-0 a ranar Asabar, inda ta lashe kofin zakarun Turai na UEFA. An buga wasan da ake sa rai a filin wasa na Wembley.

Advertisement

 

 

Advertisement

DAILY POST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending