News
Yanzu Haka Matasan Da Suke Fadan Daba A Unguwar Ja,een Sun Kulle Hanyar Gaba Daya
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Labarin Dake fitowa a yanzu haka matasan da suke fadan daba a yankin ja,een sun kulle hanyar gaba daya dai dai gidan man Aliko.
Wannan ya nuna cewa mutanen da zasuje Zawachiki, da Dorayi, da sabon titi da kuma hanyar Madobin sai dai su hakura ko su canza hanya kasancewar hanyar a toshe take.
Rundunar Yan Sanda Sun Samu Nasarar Cafke Matasa 16 Dake Harkar Fadan Daba Unguwanne Kano
Haka ma masu zowa daga madobin zuwa cikin gari da masu zowa 6angaren sabon titi sai dai su shigo ta cikin unguwanni Dake 6angaren gurungawa.
Shima wani mazaunin Unguwar ta ja’en wanda ya nemi a sakaye sunansa ya tabbatar da cewa a yanzu haka an Kara kashe mutum 2 yayin da mutune Maza da Mata ke cigaba da hijira daga Unguwar zuwa cikin gari domin tsira da rayukansu bayan harbe harben da ake a yankin yanzu haka.
Ya kuma yi kira ga hukumomi da masu ruwa da tsaki da su kawo musu daukin gaggawa gudun yaduwar abin anan gaba.
