News
Shugaban Jam’iyyar APC na kasa , Dr. Ganduje yayi rashin surukar sa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban jam’iyyar APC mai mulkin Nigeria Dr abdullahi Umar ganduje ya yi rashin mahaifiyar matarsa wato surukar sa Hajiya Asiya Muhammad Gauyama.
Hajiya Asiya Muhammad Gauyama ta rasu a safiyar ranar Litinin.
A wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na shugaban kasa Edwin Olofu ya fitar, ta bayyana marigayiya Hajiya Gauyama a matsayin mahaifiya mai daraja, wanda rayuwarta ke da nasaba da sadaukar da kai ga iyali, al’umma da kuma imani.
Olofu ya ce za a yi sallar jana’izar Hajiya Asiya Muhammad Gauyama a yau, da karfe biyu na rana, a gidan Dr. Abdullahi Umar Ganduje da ke kan titin Miyangu jihar Kano.
“Cikin alhini da alhini ne muke sanar da rasuwar Hajiya Asiya Muhammad Gauyama, mahaifiyar Farfesa Hafsatu Abdullahi Umar Ganduje, uwargidan shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje. Ganduje CON.
Sanarwar Jana,izar Tata ta cigaba da cewa “Hajiya Asiya Muhammad Gauyama mace ce mai mutuƙar daraja, wacce rayuwarta ke da alaƙa da sadaukar da kai ga iyali, al’umma, da imani.
Hakika rasuwar hajiya babban Rashi ne baga iya danginta kaɗai ba har ma ga duk wanda ya santa kuma yake ƙaunarta.
“Allah ya jikan Hajiya Asiya Muhammad Gauyama da rahama yasa aljannar firdausice makoma da baiwa iyalanta hakurin rashin ta
