Connect with us

News

Shugaba kasa Bola Tinubu ya nada fitaccen dan jarida Bello a babban mukami

Published

on

 

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin Mista Olatunji Bello a matsayin sabon babban jami’in gudanarwa Kuma Mataimaki ga hukumar kula da gasar masu sayayya ta tarayya wato (FCCPC).

Advertisement

A Wata sanarwa daya fitar mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan kafafen yada labarai dAjuri Ngelale a ranar Litinin, ta ce majalisar ta amince da nadin.

 

Advertisement

Kafin baiwa Bello mukami Shi ne tsohon sakataren gwamnatin jihar Legas kuma ya yi digiri na biyu a fannin shari’a da diflomasiyya a jami’ar Legas. Kuma Ya yi karatun lauya a jami’a guda kuma an kira shi zuwa Nigerian Bar domin Zama cikakken lauya a shekarar 2002.

Bello ya fara aikin jarida ne a jaridar Concord a shekarar 1985 kuma ya rike mukamin Editan Siyasa Group; da Kuma Editan Sunday Concord, kuma Edita, National Concord.

Advertisement

Shi ne wanda ya yi nasara a Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Alfred Friendly ta Amurka kuma an nada shi Shugaban Hukumar Edita na Jaridun THISDAY a 2001.

Ya kuma taba rike mukamin kwamishinan muhalli a karkashin gwamnatoci daban-daban a jihar Legas.

Advertisement

A cewar sanarwar, shugaban na sa ran cewa sabon babban jami’in wannan hukuma mai muhimmanci zai tabbatar da cikar aikin hukumar na kare da inganta sha’awa da jin dadin masu amfani da Najeriya da kuma tabbatar da daukar matakan tabbatar da tsaro da inganci. na kaya da Kuma ayyuka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending