Connect with us

Politics

El-rufai Ya Karbi Bakuncin Kwankwaso’i

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

El-rufai Ya Karbi Bakuncin Kwankwaso

Advertisement

Mallam Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna, ya karbi bakuncin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, a gidansa da ke Abuja, ranar Alhamis.

El-Rufai ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa na jamiyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP), kwanaki kadan bayan ya ziyarci tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a garin Daura na jihar Katsina.

Advertisement

Shugaba Tinubu Ya Sake Neman Tsawaita Wa’adin Dokar Kasafin Kudi Ta 2023

Duk da cewa wani jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne, El-Rufai yana ta magana da ‘yan adawa a baya-bayan nan.

A watan Maris, ya ziyarci shugaban jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) na kasa a Abuja.

Advertisement

Tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) yana kan hanyarsa ta samun mukamin minista a gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu amma sai da aka sauke shi a cikin minti daya.

Bayan haka, tsohuwar ministar ya ce fita daga harkar siyasa. Sai dai ya dawo kasar ya ci gaba da rayuwarsa cikin nutsuwa har zuwa ziyarar sakatariyar jam’iyyar SDP ta kasa.

Advertisement

Da yake tsokaci bayan El-Rufai ya ziyarci Buhari, tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar wakilai ta 8, Shehu Sani, ya alakanta ziyarar da wasu jiga-jigan ‘yan siyasar Arewa suka kai wa Buhari a matsayin wani shiri na tsige Shugaba Tinubu a 2027.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending