News
EFCC ta zargi wasu kungiyoyin adawa dayin zanga- zanga- domin bata sunan hukumar
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, sanar da jama’a kan wani shiri da ta bayyana a matsayin wani shiri na wata kungiya da ba ta da tushe balle makama na tayar da zanga-zangar adawa domin yiwa hukumar zagon kasa
Ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar , Dele Oyewale, ya sanyawa hannu, ta ce kungiyar ta yi kamfen sosai a shafukan sada zumunta, inda ta dauki dubbam matasa ‘yan Najeriya, ciki har da dalibai domin daukar “makamai” a kan EFCC a cikin kwanaki biyun da suka wuce
Ta ce ana ci gaba da gudanar da wannan kamfen din ne a matsayin tsayin dakatar da ayyukan hukumar musamman ta fuskar aiwatar da dokokin da suka shafi aikata laifuka ta yanar gizo. Kamar Yadda gidan television na chennals ya rawaito
“Hukumar, duk da cewa ba ta nuna adawa da zanga-zangar da ‘yan kasa ke yi ba, ta firgita da shaidun da ke fitowa da ke ba da shawarar wani babban tsari na wasu guragu da ke karkashin bincike ko gurfanar da su gaban kuliya don yin amfani da abin da ake kira zanga- zanga-
