Connect with us

News

Yan Bindiga Sun Saki Bidiyon Yayin Da Mata Da Yara Suke Kuka, Sun Yi Barazanar Kai Sabon Hari

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Wasu ‘Yan bindiga sun saki wani faifan bidiyo da ke nuna mutanen da suka yi garkuwa da su a garin Maidabino dake yankin karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina.

Advertisement

A ranar 22 ga watan Yuni wasu gungun ‘yan bindiga suka kai hari a garin Maidabino, gari na uku mafi girma a karamar hukumar Danmusa.

BIDIYO:  Wasu Matasa ‘Yan Masarautar Ƙaraye Sun Far Wa Wakilin Sarki Sunusi Ya Yin Da Ya Ziyarci Masarautar

Yayin harin, ‘yan bindigar sun kashe mutane tara tare da yin garkuwa da a kalla mutane 50, yawancinsu mata da kananan yara.

Advertisement

Daily Trust ta rawaito cewa ‘yan bindigar sun shafe lokaci mai tsawo suna cin karensu babu babbaka yayin harin da suka bayyana cewa na daukar fansa ne.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kone gidaje goma tare da kona shaguna 15 da motoci tara yayin harin da suka kai daga karfe 10 na daren ranar Asabar zuwa karfe 2:30 na safiyar ranar Lahadi.

Advertisement

Kwanaki da yawa bayan kai harin, ‘yan bindigar sun saki faifan bidiyo mai tsawon minti biyar da dakika 41 dake nuna mutanen da suka yi garkuwa da su inda suke rokon gwamnati ta zo ta kubutar da su.

A faifan bidiyon, ‘yan bindigar sun yi ikirarin cewa sun kai harin ne domin daukar fansar Matansu da ‘Ya’yansu da ‘yan sa kai, matasa ‘yan rundunar tabbatar da tsaro a jihar Katsina, suke cigaba da kashewa.

Advertisement

‘Yan bindigar sun yi barazanar cewa zasu kai wani harin a garin Danmusa nan da mako guda.

Daya daga cikin ‘yan bindigar da ya yi Magana a faifan bidiyon ya bayyana cewa ko gwamnan jihar Katsina bai isa ya kubutar da mutanen ba idan ba ta hanyar yin sulhu da su ba.

Advertisement

Mai maganar, sanye da kayan sojoji da babbar bindiga mai sarrafa kan ta, ya ce; “kun ga abinda ‘yan bijilanti suka jawo muku, kuma yanzu ba zasu iya kubutar da ku ba, ko gwamna Radda ba zai kubutar daku daga nan ba, sai dai ta hanyar sulhu.”

“Matukar kuma ba a yi sulhu da mu ba, yanzu muka fara. Zan iya bude muku wuta na kasha ku gaba daya kuma babu abinda zai faru.

Advertisement

“Zamu kai hari Danmusa cikin wannan satin mai zuwa kuma zamu kawo Karin wasu mutane nan, zaku gani kuma, zaku gan su. Sannan, kafin ku bar nan, zamu kamo ‘yan bijilanti dake kare ku.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending