News
Rana Irin Ta Yau M. K. O. Abiola Ya Rasu A Ranar Da Za A Sake Shi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rana irin ta yau Shakarar 1998, Cif Moshood Kashimawo Olawale Abiola (GCFR), wanda aka fi sani da M. K. O. Abiola ya rasu ba zato ba tsammani a ranar da za a sake shi.
Rasuwarsa ta faru ne kwanaki 29 da rasuwar Janar Sani Abacha, shugaban sojan da ya daure M.K.O. Abiola.
An Nada Malam Ibrahim Rilwan Mohd A Matsayin Sabon Garkuwan Matasan Arewa
Yayin ganawa da wasu jami’an diflomasiyyar Amurka da suka hada da Thomas Pickering da Susan Rice a wani gidan baki na gwamnati da ke Abuja, Abiola, wanda shi ne ya lashe zaben shugaban kasar Najeriya a ranar 12 ga watan Yunin 1993, ya fadi ya mutu.
Shugaban mulkin soja na lokacin Janar Ibrahim Babangida ya soke sakamakon zaben.
Rice dai ta kai wa Abiola shayi ne jim kadan kafin rugujewar sa, kuma duk da hujjojin da ke nuni da cewa ta sa Abiola guba kamar yanda ake zargi . Ko da yake, wani bincike mai zaman kansa da likitoci gwamnatin Najeriya, da kungiyar likitocin Najeriya, da Canada, da Birtaniya da kuma Amurka suka yi kuma suka shaida, ya gano kwararan shaidun da suka dade suna fama da ciwon zuciya.
Abiola wanda gwamnatin mulkin soja ta Abacha ta tsare bayan ya yi yunkurin tabbatar da kansa a matsayin zababben shugaban kasar Najeriya, ya samu lambar yabo ta kasa Grand Commander of the Order of the Federal Republic (GCFR), lambar girmamawa da aka baiwa shugabannin Najeriya kadai. , bayan mutuwarsa a ranar 6 ga watan Yuni, 2018, a Lokaci Shugaba Muhammadu Buhari.
An kuma sauya ranar dimokradiyyar Najeriya daga ranar 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni domin karrama shi.
