News
Yar Maƙwabta :An Gurfanar Da Faston Da Ya Yi Lalata Da Yarinya ‘Yar Shekara 10 A Kotu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
An gurfanar da wani limamin Kirista a kotu, bisa tuhumar sa da zargin yin lalata da ƙaramar yarinya ‘yar shekara 10, har ya fasa ta.
Ɗan sanda mai gabatar da ƙara ya shaida wa kotu cewa wanda ake zargin mai suna Francis Ogu, ya aikata fyaɗe kan yarinyar a ranar 27 ga Yuni, a gidan sa.
Shugaban Tinubu Zai Gana Da Ƙungiyoyin Ƙwadago Kan Mafi Ƙarancin Albashi
An gurfanar da Shi ranar Laraba a Kotun Shari’ar Laifukan Fyaɗe da Cin Zarafi a garin Awka, Jihar Anambra.
‘Yan sanda su na cajin Ogu mazaunin ƙauyen Umuike a Awka, Jihar Anambra.
‘Yar sanda mai gabatar da ƙara, Chinyere Okechukwu ya shaida wa kotu cewa laifin da fasto Ogu ya aikata, ya saɓa wa Sashe na 35(2) na Dokar Kare Haƙƙin Ƙananan Yara ta Jihar Anambra, ta shekarar 2004.
Sai dai wanda ake zargin ya ɗauki lauya, wanda ya shaida wa kotu cewa wanda ake zargin bai aikata laifin da ake tuhumar sa ba.
A hukuncin da ta yanke, Mai Shari’a Genevieve Osakwe ta bada belin wanda ake tuhumar kan kuɗi Naira 500,000 da kuma mutum ɗaya wanda zai tsaya masa.
Premium Times ta ruwaito cewa An ɗage sauraren shari’ar zuwa ranar 21 Ga Agusta.
