News
Shugaban Tinubu Zai Gana Da Ƙungiyoyin Ƙwadago Kan Mafi Ƙarancin Albashi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Za a sake yin zama tsakanin Shuagaba Bola Ahmed Tinubu da ƙungiyoyin kwadago kan batun mafi karancin albashi ga ma’aikata.
Jaridar ‘Tribune’, ta ruwaito cewa wani babban jami’in NLC ya ce Tinubu ya gayyaci wakilan ƙungiyoyin zuwa fadar shugaban ƙasa da ke Abuja domin tattaunawar.
Sanata Kawu Sumaila Ya Shigar Da Kuduri Domin A Raba Jihar Kano Gida 2
A ranar Alhamis ne za a gudanar da zaman inda ƙungiyoyin NLC da TUC suna kan bakansu na cewa 250,000 suke buƙatar ya zama sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan.
A kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta ce Naira 62,000 kawai za ta iya biya inda ake fatan a zaman a samu maslaha a tsakanin ɓangarorin biyu da za a yi a gobe Alhamis
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
