News
Zanga Zanga Babu Gudu Ba Ja Da Baya: Ba Ma Yunkurin Kifar Da Gwamnatin Dimokaradiyyar Najeriya —Kungiyar WAI
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kungiyar kare haƙƙin Ɗan Adam, yaƙi da rashin adalci dama bibiya akan shugabanci na gari wato War Against Injustice (WAI), ta ce su masu shirya zanga-zangar lumana ne tare da nuna rashin amincewa da matsalolin tattalin arziki, yunwa da talauci a jihar Kano.
Haka zalika kungiyar ta nisanta kanta daga yunkurin kifar da gwamnatin dimokaradiyyar Najeriya.
Muna tabbatar da aniyarmu ga ka’idodin dimokuradiyya da bin doka. Ba za mu goyi bayan duk wani aiki da ke nufin sauya tsarin mulki ta hanyar tashin hankali ko rashin bin tafarkin demokradiyya ba.
Muna kira ga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta bayyana sunayen mutane da kungiyoyin da ke da hannu a wannan makirci, tare da daukar matakan da suka dace don dakile duk wani yunkuri na kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasarmu.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da Babban Darakta Kungiyar comrade Umar Ibrahim Umar ya turawa da Jaridar INDA RANKA
Sanarwar ta kara da cewa muna kira ga hukumar DSS da kada ta yi amfani da wannan makircin da ake zargi a matsayin dalilin dakatar da Zanga Zanga-zangar mu ta lumana da bin doka da oda.
Muna kara jaddada aniyarmu ta yin amfani da ‘yancin da kundin tsarin mulkin kasar ya ba mu na yin zanga-zanga da bayyana korafe-korafen mu cikin lumana da kwanciyar hankali.
Muna kira ga daukacin al’ummar Najeriya da su zo mu yi zanga-zangar lumana don nuna adawa da matsalar tattalin arziki da yunwa da talauci
.
