Connect with us

News

Kalaman Da Aka Yi A Kan Matatar Man Dangote Zai Tsoratar Da Masu Zuba Hunnun Jari Na Cikin gida Da Kuma Wajen Kasar.

Published

on

 

Fitaccen mai yin fashin baki a kan al’amuran yau da kullum a Nijeriya, Adamu Abubakar ya danganta kalaman da aka yi a kan matatar man ta Dangote a matsayin na batanci wanda ya ce zai shafi makomar ‘yan kasuwa masu tasowa a Nijeriya da kuma ita kanta Nahiyar Afirka.

Advertisement

An gina matatar man, wadda ita ce mafi girma a nahiyar Afirka, a wani yanki da ke wajen babban birnin kasuwanci na Legas, hamshakin attajirin nahiyar, Aliko Dangote ne ya gina ta, a kan kudi dalar Amurka biliyan 20 kuma an kammala ta ne bayan shafe shekaru da dama da aka fuskanci jinkiri.

Ka Cire Tallafin Fetur, Ka Haddasa Tsadar Rayuwa, Ai Kuwa Ba Za Ka Hana Mutane Zanga-zangar Ba’ —Ƙungiyar Afenifere

Zata iya tace ganga 650,000 a kowace rana (bpd) kuma zata kasance mafi girma a Afirka da Turai idan ta kai ga cikakken karfinta a wannan shekara ko shekara mai zuwa.

Advertisement

shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote; ya mayar da martani mai gauni a kan kalaman Shugaban Hukumar ta Kula da Harkokin Sarrafawa da Tacewa da kuma Sufurin Mai a Nijeriya (NMDPRA).

Ya mayar da martanin, yayin ziyarar da wasu ‘yan majalisar wakilan Nijeriya; suka kai matatar ciki har da shugaban majalisar, Hon Abbas Tajuddeen da mataimakinsa Hon Kalu.

Advertisement

Da farko, Dangote ya bayyana wa ‘yan majalisar da ma sauran ‘Yan Nijeriya cewa, idan ba a yaba musu ba ai ba a kushe su ba, domin su kadai suka yi hobbasar gina matatar mai karfin tace gangar mai 650,000 a kullum ba tare da samun wani tallafi daga gwamnati ba. “

Dangote ya kuma kara tabbatar da sahihancin man da suke tacewa na dizel “domin wadanda suka saya sun sake dawowa suna so daga sassa daban-daban na duniya. Zuwa yanzu matatarmu ta fitar da manta zuwa wasu kasashen Tarayyar Turai da Singapore da Lome.

Advertisement

Dangote ya yi mamakin dalilin da ya sa wata hukuma ta daidaita al’amura kamar (NMDPRA) da ya kamata ta kare masana’antun cikin gida amma kuma ta koma tana hantararsu har ma da yin karya a kafofin watsa labarai don tabbatar da bukatar ci gaba da shigo da gurbataccen man fetur a cikin kasa.

“Ina kira gare ku (majalisa) da ku kafa kwamitin da zai dauki samfura a gidajen mai, mu dauki namu samfurin, domin dole ne in gaya muku cewa duk takardun tantance sahihancin mai da mutane ke yawo da su na bogi ne. Ina dakunan gwaje-gwajen da aka gudanar da binciken? Ta yin haka, za ku iya gaya wa ’yan Nijeriya ainihin gaskiyar da suka cancanci su sani. Kushe kasuwancin wani kamfani daga hukumar daidaita al’amura da ta kamata ta kare kamfanin abin bakin ciki ne da takaici

Advertisement

Dangote ya fito karara ya kalubalanci hukumar (NMDPRA) da ta bayyana ingancin man da ake shigo da su daga kasashen waje, yayin da ya yi kira da a tantance ba tare da nuna son kai ba domin sanin abin da zai dace da muradun ‘Yan Nijeriya. “Muna samar da dizal mafi kyau a Nijeriya. Abin takaici ne a ce maimakon a kare kasuwancinmu, amma mai ba da kulawa kuma yana yi masa zagon kasa. Kofofinmu a bude suke ga hukumar don gudanar da gwaje-gwaje a kan samfuranmu a kowane lokaci; gano gaskiyar lamari tare da bayyana wa jama’a ne mafi muhimmanci a gare mu. Zai yi kyau ita hukumar (NMDPRA) ta nuna dakin gwaje-gwajenta ga duniya domin ‘yan Nijeriya su rabe tsaki da tsakuwa. Babban abin da muke fatan gani shi ne Nijeriya ta bunkasa, saboda muna da karancin ci gaba.

“Shugaban majalisa da sauran membobi, kun ga sakamakon gwajin sahihancin man da aka yi. Na yaba da wannan hikima taku wajen zuwa gidajen mai ku dauki samfurin main a matatarmu. Namu ya nuna akwai sinadarin sulfo ppm 87.6, akalla dai 88, yayin da na wasu kuma ya haura ppm 1,800. Duk da cewa Hukumar NMDPRA ta amince wa matatun main a gida su samar da mai da zai kunshi sidarin sulfo 650 har zuwa Janairun 2025, kamar yadda ECOWAS ta amince, namu bai kai haka ba, zuwa mako mai zuwa, mun sha damarar samar da man da yake kunshe da sulfo ppm 10 kawai, domin ya yi daidai da ingancin da ake bukata a Tarayyar Turai. An tsara cewa man da za a shigo da shi ka rya zarce ppm 50, amma kamar yadda kuka gani daga wasu gidajen mai, da ‘yan kasuwa suka shigo da shi, ya gaza samun sahihancin da ake bukata.” In ji Dangote.

Advertisement

Ya bukaci a rika zuwa gidajen mai kai-tsaye ana daukar samfuran man da ake son tantance sahihancinsa domin a nan ne za a samu asalin man da ake shigo da shi, yana mai cewar, “na yi ammanar Farouk Ahmed ya yi magana ne ba tare sanin yadda matatarmu take ba. Mun yi nasarar fitar da dizal da man jirgi zuwa Turai da yankin Asiya kuma ba mu samu wasu korafe-korafe ba. A hakika ma, wadanda suka saya sun sake dawowa suna son kara sayen man namu,” ya bayyana.

Fitaccen mai yin fashin baki a kan al’amuran yau da kullum a Nijeriya, Adamu Abubakar ya danganta kalaman da aka yi a kan matatar man ta Dangote a matsayin na batanci wanda ya ce zai shafi makomar ‘yan kasuwa masu tasowa a Nijeriya da kuma ita kanta Nahiyar Afirka.

Advertisement

A cikin wata sanarwa, da Adamu ya raba wa manema labarai ya ce, furucin da aka yi a kan matatar wani yunkuri ne kawai na salon yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa, wanda kuma ya yi daidai da cin amanar kasa.

Har ila yau, ya kara da cewa; ga ‘yan kasuwa masu tasowa a Nijeriya da kuma wadanda ke yankunan Afirka, wannan matatar mai ta Dangote, tamkar madubi ne da zai haskaka musu hanya tare da kara musu karsashi, wajen cimma nasara a harkokin kasuwancinsu.

Advertisement

“tamkar wani yunkuri ne na son yi wa dimbin ‘yan Nijeriya kafar ungulu, musamman idan aka yi la’akari da dimbin matasan da za su samu aikin yi a wannan matatar man fetur ta Dangote.

“Matatar man ta Dangote, masana’anta ce wadda za ta sama wa ‘yan Nijeriya da sauran ‘yan Afirka alkibla mai dorewa tare kuma da samar musu ci gaba ta bangarori daban-daban.” In ji shi.

Advertisement

Haka zalika, Malam Abubakar Aliyu; shi ma ya kalli al’amarin a matsayin wata babbar barazana, musamman ga masu zuba jari a Nijeriya, domin kuwa a cewarsa; akwai alamun da ke nuna ana yi wa masu zuba hannun jari zagon kasa, domin abin da ake yi wa Dangote; zai tsoratar da masu zuba hannun jari na cikin gida da kuma na wajen kasar.

Aliyu ya kara da cewa, babu shakka hakan na iya yin matukar illa ga tattalin arzikin saboda idan har ba a zuba hannun jari ba; dole ne ya kasance ana fitar da kudaden kasar waje, domin sayo kayayyakin da za a yi amfani da su.

Advertisement

 

Tun bayan zargin matatar man fetur ta Dangoten da hukumomin ke yi, na fitar da man dizel mara inganci; wanda kuma ta musanta ta hanyar gudanar da gwaji a gaban wasu daga cikin ‘yan majalisar tarayya a ranar Asabar da ta gabata, wannan ne karo na farko da bangaren gwamnatin tarayya ta magantu, kan wannan dambarwa.

Advertisement

Rahotanni na nuni da cewa Idan ta fara aiki ɗari bisa ɗari za ta iya tace duk man fetur da ake buƙata a Najeriya har ma a samu rara da za a fitar zuwa wasu ƙasashe a kullum.

An tsara ta yadda za ta iya sarrafa nau’uka daban-daban na ɗanyen mai daga ƙasashen Afirka da na ƙasashen Gabas ta tsakiya da yankin Amurka.

Advertisement

Matatar tana da manyan tankuna 177 waɗanda za su iya ɗaukar mai da yawansa ya kai lita biliyan 4.742.

Idan ba a manta ba, Dangote ya koka kan yadda kamfanonin waje ke kin sayar wa da matatarsa danyen mai, domin fara tacewa da sayarwa a cikin gida Nijeriya.

Advertisement

Sakamakon wannan rikici dai, rahotanni, sun tabbatar da cewa; a halin yanzu Dangote ya karkata akalarsa wajen sayo danyen man daga kasashen Libiya da Angola, domin tace man fetur da za su fara fitarwa kasuwa a watan Agustan wannan shekara da muke ciki.

Duk da haka, ya sha alwashin ci gaba da gwagwarmaya kamar yadda ya saba, “kusan duk tsawon rayuwata gwagwarmaya nake yi. Na yi Imani da Allah, don haka babu wanda nake jin tsoro, zan ci gaba da gwabzawa,”

Advertisement

in ji Dangote a wani faifan bidiyo.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending