News
Ka Cire Tallafin Fetur, Ka Haddasa Tsadar Rayuwa, Ai Kuwa Ba Za Ka Hana Mutane Zanga-zangar Ba’ —Ƙungiyar Afenifere
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Ƙungiyar Kare Muradin Yarabawa Zalla ta Afenifere, ɓangaren shugabancin Ayo Adebanjo, ta bayyana cewa ta na goyon bayan fita a yi zanga-zanga kwanaki 10 da ake shirin farawa daga ranar 1 ga Agusta zuwa 10 ga Agusta.
Kakakin Yaɗa Labaran Afenifere ɓangaren Ayo Adebanjo, Falmata Daniel ne ya bayyana cewa za a fita zanga-zanga saboda yadda Shugaba Bola Tinubu ya ɗora tattalin arzikin Najeriya a kan hanyar da ba ta ɓullewa, sai dai ta jefa ƙasar nan cikin masifar raɗaɗin tsadar rayuwa.
Yoyon Fitsari: An Yi Wa Mata 50 Aiki Kyauta Da Tallafi A Kano
Sakataren Yaɗa Labarai na Afenifere, Justice Faloye ne ya bayyana haka.
“Afenifere ba ta shirin shiga zanga-zanga, amma fa muna goyon bayan duk wanda zai fito ya nuna damuwar sa kamar yadda ‘yancin ɗan Adam ya ba shi damar fitowa ya yi.
“Saboda Afenifere ta sha gargaɗi kan makauniyar hanyar da wannan gwamnati ta ɗora tattalin arzikin ƙasa. Idan ka ci gaba da cire tallafin fetur, kuma ta haifar da tsadar rayuwa, to ai kuwa babu yadda za a yi ka hana mutane fitowa. Ba za ka iya tausasa zukatan mayunwata ka ce wai su zauna a gida ba.” Inji Faloye.
Afenifere ɓangaren Ayo Adebanjo sun ɓalle daga Afenifere da ke ƙarƙashin Reuben Fasoranti daidai lokacin gabatowar zaɓen 2023, saboda su na goyon bayan ‘yan takarar shugaban ƙasa daban-daban.
Yayin da ɓangaren dattijo Fasoranti ke goyon bayan APC da ɗan takarar ta Bola Tinubu, su kuma ɓangaren Ayo Adebanjo sun goyi bayan jam’iyyar LP da ɗan takarar ta Peter Obi.
Dattijo Adebanjo mai shekaru 96 a duniya, ya yi zargin cewa Fasoranti mai shekaru 98 a duniya nauyin shekaru sun yi masa yawa, saboda haka yanzu shi ne jagora kamar yanda Jaridar premium Times ta ruwaito
Faloye a ranar Alhamis ya ce tun a baya sun sha gargaɗin gwamnatin Tinubu dangane da makahon tsarin tattalin arzikin da gwamnatin sa ta bijiro da shi, amma aka yi watsi da shawara da gargaɗin ƙungiyar. Sai gwamnati ta ce wai siyasa abin ba shawara ba.
