Connect with us

News

Yoyon Fitsari: An Yi Wa Mata 50 Aiki Kyauta Da Tallafi A Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Gidauniyar tallafa wa mata masu lalurar yayon fitsari ta Festula Foundation of Najeriya ta yiwa Mata 50 masu lalurar yoyon fitsari a Jihar Kano aikin tiyata kyauta da kuma tallafin sana’o’in dogaro da kai.

Advertisement

Daga cikinsu, an zabo mata 50 masu fama da yoyon fitsari domin yi musu tiyata kyauta a Asibitin Kwararuu na Murtala Muhammad da ke Kano.

Sufeto janar na yansanda ya amince da yin zanga zanga matsin rayuwa

A nasa bangaren Shugaban Gidauniyar tallafa wa mata masu lalurar yayon fitsari ta Festula Foundation of Najeriya Alhaji Musa Isah Baba Musa ya ce Jihar Kano ce kadai ba a aikin cutar yoyon fitsari kyauta a Duniya.

Advertisement

Haka zakika Gidauniyar ta yi bukaci gwamnatin jahar Kano ta samar da kayan aikin da za a dinga yi wa mata, ma su fama da yoyon fitsari aiki kyauta, don rage mu su radadi daga kyamar da ake nuna mu su.

Masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa aurar da yara mata a kananan shekaru na daga cikin dalilan da ke haddasa wannan cuta ta yoyon fitsari.

Advertisement

Jihar Kano na daga cikin inda wannan matsalar ta yi kamari, duk da cewa hukumomi na cewa an fara samun raguwar wannan matsala.

Mata da dama dake dauke da wannan cutar suna fuskantar mutuwar aure daga mazajen su wanda sau tari sai su zame tamkar wani abin zunde ko tsegumi cikin al’umma.

Advertisement

Alakalumman wani bincike da aka yi sun nuna Najeriya ce ta fi kowace kasa a duk fadin duniya yawan mata dake kamuwa da cutar yoyon fitsari sanadiyar auren wuri

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending