Connect with us

News

Sufeto janar na yansanda ya amince da yin zanga zanga matsin rayuwa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Sufeto Janar na ‘yansanda, Kayode Egbetokun, ya buƙaci dukkanin ƙungiyoyin da ke shirin gudanar da zangazangar a faɗin ƙasar nan da su miƙa bayanansu ga kwamishinonin ‘yansanda a jihohinsu.

Egbetokun, wanda ya zanta da manema labarai a shalkwatar rundunar yansandan ya ce an gabatar da buƙatar ne don ganin an gudanar da zanga-zangar cikin lumana tare da bayyana cewa bayanan sirri da rundunar ta samu sun nuna cewa sojojin haya na ƙasashen waje na da hannu a zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar.

Advertisement

Da yake amincewa da ‘yancin da kundin tsarin mulkin Nijeriya, ya tanada ga ‘yan ƙasa na damar gudanar da taro ko zanga-zangar lumana, inda ya bukaci dukan ƙungiyoyin da ke shirya zanga-zangar da su yi wa kwamishinan ‘yansanda cikakken bayani a jiharsu, inda ake son gudanar da zanga-zangar.

Wannan ya ce zai rage hatsarin tashin hankali da lalata dukiya ko wasu ayyukan laifuka daga masu zanga-zangar tare da biyayya ga doka ba take haƙƙin wasu ba, inda ya ce shaida cewa suna sa ido tattare da barazanar zanga-zangar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending