Connect with us

News

Me ya sa shafin ɗaukar aiki na NNPCL ya daina aiki jim kaɗan bayan buɗe shi?

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL shi ne yake tashe a kafafen sada zumunta a ranar Juma’ar nan sakamakon buɗe shafin ɗaukar aiki da kamfanin ya yi da misalin ƙarfe 12:00 na daren Juma’ar, inda kuma shafin ya daina aiki kimanin minti biyar bayan buɗe shi.

Advertisement

NNPCL dai na son ɗaukar sabbin waɗanda suka kammala jami’a da kuma ƙwararru domin cike guraban aiki a kamfanin.

Zanga Zanga Babu Gudu Ba Ja Da Baya: Ba Ma Yunkurin Kifar Da Gwamnatin Dimokaradiyyar Najeriya —Kungiyar WAI

Wannan dai za a iya cewa shi ne ɗaukar aiki na farko da kamfanin zai yi tun bayan gyaran fuska da aka yi masa a 2022.

Advertisement

Tambayoyin da jama’a da dama ke yi su ne shin me ya sa shafin ɗaukar aikin na kamfanin ya daina aiki da gaggawa? Shin rubdugun da jama’a suka yi wa shafin ne ya sa hakan? Shin rashin aikin yi ne ya sa hakan ko kuwa neman aiki me tso

ka ne?

Advertisement

Tuni dai kamfanin a shafinsa na X ya ce ya fahimci matsalar kuma ƙwararru na aiki a kai domin warware ta domin masu neman aiki su ci gaba da nema aikin.

Me ke sa shafin ɗaukar aiki ya daina aiki?

Advertisement

Injiniya Umar Saleh Gwani, wani masanin kuma mai sharhi kan fasahar zamani a Abuja ya ce dalilai biyu ne ke sa shafin intanet ya daina aiki.

“Idan aka ce Portal a bayansa akwai wasu manhajoji da dama waɗanda ke bai wa jama’a dama su shiga su yi mu’amala da wannan shafin. Tunda kuma su shafukan nan suna cikin rumbun ajiya ne wanda ake kira “databases”, kowane a cikinsu yana da iya yawan mutanen da zai iya ɗauka wato su shiga a lokaci guda wanda ake kira a Turance da “Concurrent users”.

Advertisement

Idan su waɗanda suka gina shafin sun ƙayyade cewa mutum alal misali 500 ne za su iya mu’amila da shafin a lokaci guda, to idan aka samu yanayin da suka fi haka yawa to sai shafin ya tsaya wato ya daina aiki.” In ji Injiniya Umar Saleh Gwani.

Injiniya ya kuma ƙara da cewa “na biyu kuma akwai hanya da ake amfani wajen shiga shi kansa intanet ɗin da ake kira da “bandwith”, to kowane shafi da ke kan intanet akwai abin da ake kira “server” da kowane shafi ke kansa sannan shi wannan “server” ɗin akwai taƙaitaccen bututu da ake ba shi kuma yawan “bandwith” da aka ba shi iya yawan mu’amilar da jama’a za su iya yi da shi kenan.” Kamar yadda masanin ya ƙara bayani.

Advertisement

Daga ƙarshe Injiniya Umar Gwani ya ce yana kyautata zaton cewa jama’a ne suka yi wa shafin yawa sakamakon buƙatar da jama’a ke da ita ta neman aikin.

 

Advertisement

“Ya kamata da masu tsara shafin an yi tanadin cewa ko mutum nawa ne za su shiga shafin ba za a samu matsala ba ta yadda za a ayi amfani da fasahohi da ke jure hulɗa da jama’a masu yawan gaske da ake kira ‘load balancing” ko “content delivery”.

 

Advertisement

NNPC zai soma hako danyen mai a jihar Nassarawa

Me ya haddasa saɓani tsakanin Dangote da hukumomi a Najeriya?

Advertisement

Me ya sa ƴan Najeriya ke tururuwar neman aiki a NNPCL?

Masanin tattalin arziki kuma mai fashin baƙi a najeriya, Malam Yusha’u Aliyu ya ce dalilan da ya sa jama’a ke rububin neman aiki a kamfanin NNPCL guda biyu ne:

Advertisement

 

“Na ɗaya idan ka duba alƙaluban da hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta fitar a watan Janairun 2024 dangane da yawan matasan da ba su da aikin yi ai ka ga dole ne jama’a su yi dafifi.

Advertisement

 

Abu na biyu kuma shi ne akwai matsalar ma’aikatan da ke son sauya aikin da suke yi zuwa mai tsoka irin na NNPCL. Kuma abin da hakan yake nunawa shi ne rashin daidaito a gwamnatance inda wasu ma’aikatan ba sa samun kaso ɗaya cikin biyar na abin da wasu ma’aikatan ke samu. Ka ga kuwa dole ne a samu rububi.”

Advertisement

 

Me ya sa ƴan Najeriya ke neman aiki mai tsoka?

Advertisement

Malam Yusha’u Aliyu ya ce dole ce ta sanya ƴan Najeriya neman aiki inda za su samu isassun kuɗin da za su biya musu buƙatunsu na yau da kullum.

 

Advertisement

“Shi ya sa da farko na yi magana a kan samar da daidaito tsakanin ma’aikatan gwamnati. Ba zai yiwu ba mutum wanda ya kammala digiri da sakamako mafi kyau ya ga na ƙasan shi yana aiki yana karɓar abin da ko kusa ba ya karɓa a matsayin albashi kuma idan ya ga irin wannan damar ka ce ba zai yi rububin neman ta ba.”

 

Advertisement

Masanin ya kuma lissafa dalilan da ya ce ke sanya ƴan Najeriyar neman aiki mai tsoka da ake kira “white colour job” a Turance.

 

Advertisement

Tsananin rayuwa: Mutane kan ƙoƙarin samun aiki mai tsoka domin biyan buƙatunsu da na iyalansu ba tare da sun takura ba.

Rashin haƙuri: Da dama ƴan Najeriya musamman matasa ba su da haƙurin da juriyar yin ayyukan da ba za su sama musu kuɗaɗe masu yawa ba wataƙila saboda yanayin matsin da ake ciki.

Advertisement

Gasa: Wasu mutanen kan ƙudire a ransu cewa abokina wane yana aiki a kamfani kaza kuma ya mallaki abu kaza saboda haka ni ma sai na mallaka.

Yadda za ku nemi aikin NNPCL

Advertisement

Tuni dai kamfanin na NNPCL ya ce ƙwararru na aiki domin magance matsalar da tabbatar da cewa masu neman shiga shafin sun samu nasara.

 

Advertisement

Kamfanin ya sa ranar 20 ga watan Agusta a matsayin ranar da za a rufe shafin na neman aiki.

 

Advertisement

A sanarwar aikin dai, NNPCL ya ce yana neman sabbin ƴan jami’a da kuma ƙwararru da ke da waɗannan abubuwa:

 

Advertisement

Ajin farko:

 

Advertisement

Digiri na ɗaya mai daraja ta ɗaya ko mai daraja ta biyu

Babbar difiloma mai daraja ta ɗaya

Advertisement

Digiri na ɗaya mai daraja ta uku amma tare da shaidar kammala digiri na biyu

Babbar difiloma mai daraja ta biyu tare da shaidar kammala digiri na biyu

Advertisement

Dole a kammala karatun daga jami’a ko kwalejin fasaha mai ƙima a shekarar 2019

Dole a kammala yi wa ƙasa hidima

Advertisement

Ka da mai neman aikin ya wuce shekara 28 ya zuwa ranar 31 ga watan Disamban 2024

Dole ne a mallaki dabarun sadarwa da ilimin komfuta.

Advertisement

Aji na biyu – Ƙwararru:

 

Advertisement

Digiri na ɗaya mai daraja ta ɗaya ko mai daraja ta biyu

Babbar difiloma mai daraja ta ɗaya

Advertisement

Digiri na ɗaya mai daraja ta uku amma tare da shaidar kammala digiri na biyu

Babbar difiloma mai daraja ta biyu tare da shaidar kammala digiri na biyu a fannonin ilimi

Advertisement

 

 

Advertisement

 

BBC HAUSA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending