News
Kungiyar Dalibai Ta Kasa NANS Ta Ce Zanga Zanga Babu Gudu Ba Ja Da Baya A. Ranar 1 Ga August
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kungiyar Daliban Nigeria (NANS) reshen arewa maso yamma ta ce Zanga Zanga Babu Gudu Ba Ja Da Baya 1 Ga August sabida matsalolin ilimi, tattalin arziki da zamantakewa, musamman a Jihar Kano.
Sakataren Kudi Kungiyar Comr. Ismail Ambaddi ya baiyyana hakan a yayin taron manema labarai a yau Ashirin da Bakwai ga Watan Yuli a jihar Kano
Za A Daure Duk Shugaban Karamar Hukumar Da Ya Yi Wadaka Da Kudin Kananan Hukumomi –Gwamnatin Tarayya
Ya kara da cewa cire tallafin man fetur ya haifar da karuwar kudaden karatu a jami’o’inmu dasauran manyan makarantun gaba da sakandire, wanda ya haifar da rashin zuwa Makaranta ta dalibai da yawa, ta kuma kara nauyi ga dalibai, iyalai, da rage shiga harkokin ilimi, karuwanci ya karu, kwacen waya, dakuma harkar Daba, wanda hakan na iya haifar da babbar barazana ga tsaron kasa, musamman a Jihar kano a wannan lokaci na wahalar rayuwa.
Dan haka Sashe na 39 da na 40 na Kundin Tsarin Mulkın Tarayyar Najeriya na 1999 (kamar yadda aka yi masa kwaskwarima) ya baiwa kowane mutum yancin fadin albarkacin bakinsa da yin taro na lumana ko yin cudanya da wasu don kare muradunsa.
Bugu da kari, mu a matsayinmu, za mu ba da goyon baya da kuma wayar da kan daliban Najeriya don shiga zanga-zangar lumana ta kasa baki daya, tare da yin amfani da ‘yancinsu na kundin tsarin mulkin kasar don bayyana kokensu dangane da wahalhalun da ake fama da su, da rashin aikin yi, iya biyan kudin Makaranta, dakuma yunwa a fadin kasar
Muna kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya da ta kara yawan kudade a fannin ilimi domin rage radadin wannan wahalhalu, da magance matsalolin fashi da makami, da tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a kasar.
Haka zalika ya ce ba za su yi shuru ba yayin da muke fuskantar wahala da matsin rayuwa, muna neman a dauki mataki, kuma muna bukatar hakan cikin gaggawa. Don haka, Shugaban Gamaiyar Shuwagabannin Dalibai na Jami’o’i (SUGs), zai mika bayanan tsare-tsaren mu ga SUGs da SRCs daban-daban yayin da daliban Jihar Kano za su karbi bayanan daga wajen shuwagabannin na Makaranta.
Daga karshe muna kira ga jami’an tsaro da su tabbatar da kare rayuka da dukiyoyi masu yayin zanga Zangar lumana.
