Connect with us

News

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Nemi Ganawa Da Masu Zanga-zanga

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ce gwamnati ba za ta lamunta da kowane irin tashin hankali na zanga-zangar da ake shirin yi.

Advertisement

Gwanan ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi ga ƴan kasuwa,sarakunan argajiya, da malaman addini a gidan gwamnati da ke Kano, a yau Laraba.

Zaben Kananan Hukumomi:  Za A Yi Wa ‘Yan Takara Gwajin Kwaya Kafin Ba Su Damar Tsayawa Takara A Kano

Haka kuma Gwamnan ya jaddada cewa, “ku sani zanga Zanga-Zanga ba zai kai mu ko’ina ba. Ina kira ga masu son yin amfani da ‘yancinsu na yin zanga-zanga da su guji yin duk wani abu da zai jawo barna.

Advertisement

“Mun samu sahihan bayanan sirri da ke nuna cewa wasu mutane sun yi hayar ‘yan daba domin tada fitina a jihar.

 

Advertisement

Ina tabbatar muku da cewa gwamnati ba za ta lamunci irin wadannan abubuwa ba.saboda haka shiyasa na aika, da goron gayyata ga masu son gudanar da zanga-zanga da su zo gidan gwamnati, don inji koke-kokensu mu tattauna.”

Ya bayyana kokarin gwamnatin jihar na aiwatar da manufofi da tsare-tsare da nufin inganta rayuwar ƴan kasa.

Advertisement

“Muna ƙoƙarin hadin kai a kokarinmu na samar da ingantaccen canji wanda zai samar da manufofin da ake so na zaman lafiya, ci gaba, da kwanciyar hankali a rayuwar siyasa. Duk da haka, dole ne in jaddada cewa kafofin watsa labarun sun yi mummunar tasiri ta hanyar bari a ci zarafin shugabanni, wanda ba zai taimaka mana mu cimma burinmu ba.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending