News
Zanga Zanga: An shiga ganawar sirri tsakanin Sanata Ali Ndume da shugaban jam, iyyar APC
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Sanatan dake wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dokokin kasar Mohammed Ali Ndume, a halin yanzu yana ganawa da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Taron dai yana gudana ne haka yanzu a sakateriyar jam’iyyar APC ta kasa dake Abuja.
Idan za,aiya tunawa dai a kwanakin baya ne aka tsige Sanata Ndume daga mukaminsa na babban Mai tsawatarwa a majalisar dattawa saboda sukar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan matsalar yunwa dake addabar Al, ummar nageriya
Hakan ya biyo bayan wata wasika mai dauke da sa hannun DR Abdullahi Umar Ganduje ya aikewa sakataren jam’iyyar
na kasa, Sanata Ajibola Bashiru, shi kuma ya mikawa Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya karanta kuma aka amince da ita a lokacin zaman majalisar
Kuma nan take aka maye gurbin Ndume da Sanata Tahir Monguno mai wakiltar Borno ta Arewa wato( Barno North) a matsayin babban mai tsawatarwa
Sanata Mungono ya kuma zama mataimakin shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa, wanda har yanzu Ndume ke rike da shi, kafin a dauki matakin ladabtarwa a kansa.
Tun daga lokacin ne dai magoya bayan Ndume ke ta zanga-zanga tare da yin kira ga majalisar dattawa da jam’iyyar APC da su mayar da shi kan mukamin sa na babban mai tsawatarwa a majalisar
Sai dai jaridar daily trust tace babu cikakken bayani gameda da abunda Shugaban jam iyyar APC na kasa ke tattaunawar dashi da sanatan Ali Ndumen
