News
Shin Da Gaske Gwamnatin Zamfara Ta Ware Biliyan 19 Don Sanya Wa Lawal Kayan Girki?
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin Zamfara ta karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ta ware Naira biliyan 19 don saya wa Gwamna Dauda Lawal kayan girki.
Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki na Jihar, Abdulmalik Gajam, ya bayyana wannan labarin a matsayin labarin kazon kurege a wani taron manema labarai da aka yi a Gusau.
Zaman Mutum Shi Kadai Na Wani Dan Lokaci Zai Iya Rage Masa Gajiya Da Kuma Damuwa
Gajam, ya bayyana cewa, bayanan da ake yadawa ba su da tushe, face son bata sunan gwamnan jihar kamar yanda Jaridar Leadership ta ruwaito
Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta mayar da hankali wajen rage zurarewar kudi.
Ya bukaci kafafen yada labarai da sauran masu ruwa da tsaki suke tabbatar da sahihancin bayanai kafin yadawa.
Yayin da yake jaddada aniyar gwamnatin na kasancewa mai gaskiya, Gajam ya gayyaci manema labarai su bincika tare da tabbatar da gaskiyar lamarin.
Ya yi gargadi cewa, yadawa irin wadannan bayanai marasa tushe na iya jefa jama’ar Zamfara cikin rudani.
Gajam, ya kuma sake jaddada manufofin kasafin kudin 2024, wanda ke mayar da hankali wajen samar da karin kudaden shiga, rage kashe kudi, da kuma tabbatar da gaskiya wajen fitar da kudaden jama’a.
Ya tabbatar da cewa dukkanin kudaden da gwamnati ke kashewa a yanzu yana amfanar da jama’ar jihar.
