Connect with us

News

NELFUND Ya Yi Kashedi Akan Shafin Yanar Gizo Na Yaudara Da Ke Ikirarin Bayar Da Tallafin Bizar Kasar Waje

Published

on

NELFUND Ya Yi Kashedi Akan Shafin Yanar Gizo Na Yaudara Da Ke Ikirarin Bayar Da Tallafin Bizar Kasar Waje

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Asusun ba da lamuni na ilimi na Najeriya (NELFUND) ya gargadi jama’a game da wani shafin yanar gizo na yaudara da ke ikirarin bayar da tallafin bizar kasar waje, ta hanyar amfani da suna da tambarin NELFUND.

Advertisement

Mista Nasir Ayitogo, shugaban hulda da jama’a ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Talata a Abuja.

Hukumar FRSC Ta Tabbatar Da Mutuwar Mutane 16 A Wani Haɗarin Mota A Hanyar Legas

Ayitogo ya ce shafin yanar gizon, da ake yada shi a shafin Facebook, ya tura masu amfani da shi zuwa wani shafi mai suna labari.com.ng.

Advertisement

Ya bayyana cewa NELFUND ba ta da alaƙa da irin wannan shafin yanar gizon ko wani tsari makamancin haka.

“Manufar NELFUND ita ce zata bada lamuni na ilimi ga daliban Najeriya da suka cancanta don ci gaba da ayyukansu na ilimi a cikin Najeriya.

Advertisement

“NELFUND bata bayar da tallafin visa ko ayyuka masu alaƙa da hakan , kuma duk wani da’awar akasin haka gabaɗaya karya ce kuma yaudara ce.”

Ya kara da cewa shafin yanar gizo na yaudara yana amfani da sunan NELFUND da tambarinsa ba tare da izini ba don yaudarar jama’a, kuma asusun ya shawarci kowa da kowa da ya yi taka tsantsan tare da nisantar da shafin ko bayar da bayanan sirri.

Advertisement

Ayitogo ya ce NELFUND na daukar matakan gaggawa don shawo kan lamarin, inda ta kai rahoton lamarin ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da bincike.

 

Advertisement

(NAN)

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending