Connect with us

News

Kungiyar ASUU Ta Fitar Da Sanarwar Tafiya Yajin Aiki Nan Da Kwanaki 21

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kungiyar ASUU Ta Fitar Da Sanarwar Tafiya Yajin Aiki Nan Da Kwanaki 21

Advertisement

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU) ta fitar da sanarwar tafiya yajin aiki nan da sati Uku idan har ba a biya musu bukatunsu ba.

Sanarwar ta fito ne a yayin da aka gudanar da taron majalisar zartarwa ta kasa, wanda ya gudana a jami’ar Ibadan (UI), kuma ana sa ran mika kwafin ga kungiyoyin kwadago da ma’aikatun ilimi na tarayya.

Advertisement

Likita ya,yi sanadiyyar mutuwar Yarinya Yar shekaru 9 ta hanyar yi mata  fyade 

Kungiyar ta ce ta baiwa Gwamnati Wa’adin ne domin matsa lamba don ganin an biya musu bukatunsu da kuma hana datse karatu a cibiyoyin ilmi da ke faɗin ƙasar.

“Yanzu dai wa’adi muka ba gwamnati Mun ba ta kwanaki 21, daga nan zamu tsunduma yajin aikin.

Advertisement

“Dalilin fitar da sanarwar saboda yin hakan doka ce a karkashin dokokin aiki, don haka muna kokarin ganin mun yi komai yadda doka ta tanada,” in ji majiyar.

In ba a manta ba WikkiTimes ta ruwaito cewar, ASUU ta yi barazanar shiga yajin aikin saboda rashin aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma tsakanin ta da gwamnatin tarayya.

Advertisement

Inda a ranar 26 ga watan Yuni ne Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya gayyaci kungiyoyin zuwa wani taron tattaunawa kan batutuwan da suka shafi jami’o’i da kuma dakile yajin aikin da suka shirya yi.

Sai dai Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, Shi ne ya bayyana cewa shiru har yanzu an kasa aiwatar musu da yarjejeniyoyin da aka kulla da gwamnatin tarayya.

Advertisement

”Shugaban ya ƙara da cewa wasu daga cikin bukatun da suke nema a biya musu sun haɗa da rashin biya musu bukatun da suka nema tun a shekarar 2009.Ya ce an shafe fiye da shekaru shida ana kulla yarjejeniyar, amma har yanzu an kasa haifar da Ɗa mai ido.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending