Connect with us

News

Dalilin Da Yasa Na Mika Takardar Barin Aiki Ga Shugaba Tinubu – Shugaban Hukumar Leƙen Asiri Ahmed Rufai

Published

on

images 17 1

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Da yammacin ranar Asabar ne shugaban hukumar leken asiri ta kasa (NIA), Ahmad Rufai Abubakar, ya mika takardar yin murabus daga mukaminsa ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, a fadar gwamnatin tarayya.

Da yake magana da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawar sa da Shugaba Tinubu, Ahmed Rufai ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin aiki ne saboda wasu daliali masu nasaba da harkokin iyali, yana mai karfafa cewa ba matsala ce tasa ya ba ajiye aikin ba.

Rundunar Ƴan Sanda Ta Tabbatar Da Ceto Ɗaliban Likitanci 20 Da Aka Sace 

Ya bayyana godiyarsa bisa fahimtar da shugaba Tinubu ya nuna a yayin da ya mika masa takardar barin aiki tare da bayyana cewa abotar da ke tsakaninsu za ta cigaba.

Shugaban na NIA mai barin gado ya ci alwashin cewa zai cigaba da saka ido tare da bayar da gudunmawar sa ga harkokin da suka shafi tsaron kasa duk da ya bar aiki.

“Akwai dalilai da dama da zasu sa mutum ya ajiye aiki, wasu dalilan sun shafi rayuwar mutum ne, a bangarena babu wani babban dalili, sannan alakar da ke tsakanina da shugaban kasa zai cigaba.

Advertisement

“Na tattauna da shugaban kasa, ya fahimce ni sosai kuma na yi masa alkawarin cewa zan cigaba da nuna damuwa a kan harkokin da suka shafi tsaron kasa,” a cewar sa.

Da aka tambaye shi ko menene ra’ayin shugaba Tinubu dangane da murabus din da ya yi, Ahmed Rufai ya bayyana cewa, “wannan ba hurumina bane na yi magana a kai, watakila sai dai ku ji daga bakinsa ko kuma mai bashi shawara a kan harkokin tsaro.”

A shekarar 2018 ne tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya fara nada Ahmed Rufai a matsayin shugaban NIA kafin daga bisani ya saka kara sabunta nadinsa a shekarar 2021.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending