News
MATSALAR TSARO: Rundunar Ƴan Sanda Ta Kama Matar Da Ke Safara Harsashi A Galan Ɗin Manja
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar ƴan sanda reshen jihar Nasarawa ta yi nasarar cafke wata mata mai suna Hauwa Sani ɗauke da galan ɗin Manja shaƙe da harsashin jiragen yaƙi kimanin guda dari da ashirin da hudu da kuɗi N78,500 a hanyar Katsina.
Kakakin rundunar ƴan sanda jihar Ramhan Nansel, ya ce an kama matar ne tare da yarinya ƙarama yar shekara 2 a kauyen Doro na jihar Katsina kamar yanda Jaridar WIKKI TIMES ta ruwaito
Nansel ya ce jami’an ‘yan sandan da ke aiki da sashen Keffi sun yi nasarar kama ta ne bisa sahihin bayanai da suka samu.
Ya ce wacce ake zargin ta karbo kayayyakin ne daga kauyen Rafin Sanyi da ke karamar hukumar Doma, jihar Nasarawa, zuwa jihar Katsina.
“A ranar 23/8/2024 bisa samun sahihan bayanai, jami’an ‘yan sanda yankin Keffi suka yi nasarar kama wata Hauwa Sani ɗauke da karamar yarinya a ƙauyen Doro, jihar Katsina.
“An sake ta ɗauke da alburusai dari da ashirin da hudu (124) maƙare a cikin galan din manja, wayar hannu daya, da kudi Naira78,500”.
“Bincike na farko ya nuna cewa wanda ake zargin ta karbo kayan ne a kauyen Rafin sanyi da ke karamar hukumar Doma a jihar Nasarawa ta kuma koda su a cikin galan din manja ta,” cewar Nansel.
Ya ci gaba da cewa, yanzu haka dai an mika wacce ake zargin zuwa sashen tattara bayanan sirri na rundunar ƴan sanda da ke Abuja domin ci gaba da bincike.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
