News
Sabon kwamishinan Yan Sanda na Akwai Ibon Ya Rasu bayan Anyimasa Aikin Kansa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
wamishinan Yan Sanda na jihar Akwa Ibom Waheed Ayilara ya rasu bayan watanni shida da kama aiki
Ayilara, ya zama kwamishinan ƴan Sanda na jihar a watan Fabarairu, ya rasu ne a yayin da ake yi masa aiki a asibitin jihar Legas.
Jaridar Daily Trust ta rawaito Kwamishinan ya rasu ne awanni kadan bayan halartar bikin kammala aiki da na zagayowar ranar haihuwa ga wasu manyan jami’an ‘Yan Sanda da ya gudana a Jahar Legas a jiya Laraba.
An rawaito cewa , ya rasu da safiyar yau Alhamis a asibitin koyarwa na jihar Legas inda likitoci ke yajin aiki.
Mamacin dai ya na fama da matsalar ciwon Kansa, inda aka yi masa aiki a safiyar ranar.
Sai dai ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan Sandan Legas, Benjamin Hundeyin ba a daidai lokacin da ake hada rahoton.
