Connect with us

News

Bamu Hana Ƴan Ƙasa Da Shekara 18 Rubuta Jarrabawar NECO Da WAEC Ba  —Gwamnatin Tarayya

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta bayyana cewa ba ta hana daliban da ba su kai shekaru 18 ba da rubuta jarabawar kammala sakandare ta Afirka ta Yamma, WASSCE, da Hukumar Jarabawa ta Kasa, NECO ba

Advertisement

Karamin Ministan Ilimi, Dakta Yusuf Sununu, ne ya bayyana hakan a Abuja a yau Juma’a yayin da ya ke gabatar da tambayoyi daga ƴan jarida a wani taron tunawa da ranar karatu ta duniya ta 2024 (ILD).

 Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Amince Da Ƙudirin Ƙirƙiro Hukumar Inganta Karatun Tsangaya

Sununu ya ce rashin fahimtar da jama’a su ka yi da kuma fahimtar da basu yi wa Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman ba abu ne mai matukar takaici.

Advertisement

Ya ce a zahiri ministan ya na magana ne kan shekaru 18 na shiga manyan makarantu kamar yadda aka yi a tsarin ilimi na 6: 3: 3: 4.

“Mun yarda cewa za mu dauke shi a matsayin aiki mai gudana. Majalisar kasa tana aiki kuma muna aiki.

Advertisement

“Abin mamaki ne a ce wata jami’a a kasar nan ta ba yara ƴan shekara 10, 11 da 12 gurbin karatu. Wannan ba daidai ba ne.

“Ba mu na cewa ba zai yiwu ba, mun san za mu iya samun hazikan dalibai wadanda suke da IQ na manya ko da suna shekara 6 da 7, amma wadannan kadan ne.

Advertisement

“Dole ne a samar da doka, kuma ma’aikatar tana duban samar da ka’ida ta yadda za a gano yaro mai hazaka, don kada iyaye su ce muna hana ‘ya’yansu dama.

 

Advertisement

DAILY NIGERIAN

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending